
Hasumiyar Babila/The Tower of Babel (Genesis 11: 1-9)
هَوُسَ / Yaren Hausa (Hausa)
- A lokacin, harshen mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma
ɗaya ce.
- Sa'ad da mutane suke ta yin ƙaura daga gabas, sai suka sami
fili a ƙasar Shinar, suka zauna a can.
- Sai suka ce wa juna, "Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai."
Suka yi aiki da tubali maimakon dutse, katsi kuma maimakon lāka.
- Sai suka ce, "Ku zo, mu gina wa kanmu birni, da hasumiya wadda
ƙwanƙolinta zai kai can cikin sammai domin mu yi wa kanmu suna,
domin kada mu warwatsu ko'ina bisa duniya."
- Ubangiji kuwa ya sauko ya ga birnin da hasumiyar da 'yan adam suka gina.
- Ubangiji kuwa ya ce, "Ga su, su jama'a ɗaya ce, su duka kuwa
harshensu guda ne, to fa, ga irin abin da suka fara yi, ba abin da za su
shawarta su yi da zai gagare su.
- Zo mu sauka, mu dagula harshensu, domin kada su fahimci maganar juna."
- Haka kuwa daga wurin Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya, sai
suka daina gina birnin.
- Domin haka aka kira sunan wurin Babila, domin a nan ne Ubangiji ya
dagula harshen dukan duniya, daga nan ne kuma Ubangiji ya warwatsa su
ko'ina bisa duniya.
Information about Hausa |
Useful phrases in in Hausa |
Tower of Babel in Hausa
Tower of Babel in Chadic languages
South Giziga,
Hausa,
Mafa
Other Tower of Babel translations
By language |
By language family
Learn Chinese Characters with the Omniglot Chinese app